Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock, ta ce wannan tunanin ba shi ne mafita ba, kuma kada a yi tsammanin irin wannan matakin zai dakatar da tabkokin yakin Rasha ba.
Sama da rabin iskar gaz da Jamus ta dogara da shi tana shigar da shi ne daga Rasha, sannan kashi 42% na man fetur din ta da kuma kwal daga Rasha ne.
Rikicin na Rasha da Ukraine, a wannan Litinin rikicin kara ya girgiza kasuwannin duniya musamman farashin man fetur, zinari da kuma mummunar faduwar hannayen jari a Asiya.
342/